Gwamnatin jihar Barno zata samar da makarantar marayu

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin jihar Borno ta kashe Naira Biliyan daya da Miliyan 200 wajen sayen wasu rukunun gidajen mallakar babban bankin Najeriya, wanda ake kira CBN quarters.

Gwamnatin jihar Borno tace za ta mayar da gidajen makarantar marayun da suka rasa iyayensu sakamakon rikicin ‘yannkungiyar Boko Haram. Kwamishinan ma’aikatar ayyuka da sufuri na jihar Alhaji Adamu Lawan, shine ya shaidawa manema labarai a garin Maiduguri.

Kwamishinan yace yanzu haka gwamnatin ta kammala biyan kudin rukunin gidajen da ake shirin kafa makaranta, don taimakawa marayun da ‘yan Boko Haram suka hallaka iyayensu, don tabbatar da ganin sun sami ilimin zamani da na addini.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Yace zasu kebe wani bangare cikin
rukunin gidajen don ya zama gidajen matan da ke kula da yaran.

Haka kuma kwamishinan ya yi karin
haske game da gyaran hanyar da ta tashi daga garin Maiduguri zuwa Gamborin Gala wadda kuma ta dangana da kasar Kamaru, da cewa yanzu haka sun fara gyaran hanyar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.