Good luck ebele Jonathan ya sha Sammaci

0 4

Click to subscribe my channel

Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zama a Abuja ta yi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sammaci domin ya zo ya bada sheda a shari’ar da ake yi wa tsohon
sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Olisa Metuh.

Wannan ya biyo bayan bukata da lauyoyin Metuh suka shigar a kotun, wanda kuma alkalin kotun, mai sharia Okon Abang ya amince.

Jaridar Punch ta rahoto cewa sai da aka kammala sauraran karar a jiya Litinin tukunna lauyoyin suka shigar da wannan bukata.

Rahotan ya bayyana cewa bayyanar Goodluck a kotun gobe Laraba ya ta’allaka ne akan yiwuwar mika mashi takardar sammacin a jiya
ko yau Talata.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Da yawa a cikin shaidun Metuh da suka gabata
a kotun dai sun kafe akan cewa da amincewar tsohon shugaban kasar aka aikawa Metuh  Naira miliyan 400 daga ofishin tsohon mai
bada shawara akan harkokin tsaro.

Lauyan metuh, dakta Onyechi Ikpeazu (SAN) ya fadawa alkalin kotun cewa sai da ya aikawa Goodluck wasikar gayyata domin ya zo ya bada sheda amma bai ji daga wajen tsohon shugaban kasar ba tun wannan lokaci.

©hausa.naji

Click to subscribe my channel