Fadar Shugaban Najeriya Ta Musanta Raderadin Wargaza Majalisar Zartaswa

0 8

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fadar shugaban Najeriya Muhammad Buhari ta fito tace ba gaskiya ba ne raderadin cewa zai yiwa majalisar zartaswarsa garambawul har ma wasu kafofin labarai sun rubuta zai sauke ministoci akalla goma.

Kakakin shugaban Garba Shehu ya shaidawa Muryar Amurka a wata tattaunawa da yayi ta musamman cewa abun da ake yayatawa babu kashin gaskiya ciki.

Yace su karan kansu sun karata
maganar ce a kafofin labaru. Ya kara da cewa a lokacin da suke taron majalisar zartaswa shi shugaba Buhari ya fada cikin raha cewa ya karanta cewa zai canza ministoci.

Malam Garba yace idan shugaban kasa wanda yake da ikon nadawa da tubewa bai san da maganar ba don haka bai san inda maganar ta samo tushe ba.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Malam Garba yace idan shugaban ya shirya zai yiwa majalisar garambawul zai sanar da jama’a.

Amma wasu ‘yan gani kasheni na
shugaban suna da ra’ayin a yiwa
majalisar garambawul. Ciroman BakanbDaura, wani dan gani kashenin Buhari yace idan Allah ya sa Buhari ya yiwa majalisar garambawul to lallai ya farga
saboda duk wadanda ya tara yanzu ba wadanda zasu taimakeshi ba ne injishi.

Inji Bakan Daura mutanene da sua
aikata cin hanci da rashawa da
almundahana. Yawancinsu ba mutanen da zasu taimaka masa ba ne.

A nashi bangaren malamin Islama
Useni Zakariya yace addu’a shugaban ke bukata ba garambawul a gwamnati ba saboda babu abun da zai faru sai Allh ya yadda.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.