Fada maiduguri ta government zata koma bama

0 2

Click to subscribe my channel

Gwamnan jahar Borno Kashim Shettima ya
hanke hukuncin dauke gwamnatinsa cancak
daga garin Maiduguri ya mayar da ita garin
Bama domin ya jagoranci sake gina garuruwan
da rikicin Boko haram ya lalata.
Ya yanke wannan shawara ne ganin yadda ‘yan
gudun hijira ke dari darin komawa Bama da
garuruwan da ke kewaye da shi wadanda
sojojin Nijeriya suka kwato daga hannun ‘yan
Boko Haram.
A hirar da ya yi da kafar yada labarai ta Muryar
Amurka, gwamnan ya bayyana cewa
gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan sake gina
wasu daga cikin garuruwan, kuma ta na ci
gaba da yin hakan har sai gaba daya ‘yan
gudun hijiran jahar sun samu matsuguni.
Ya kara da cewa, washegarin sallah zai
kwashe inashi-inashi ya koma Bama da zama
da shi da gwamnatinsa, inda zai sa ido har sai
ya ga an sake gina Bama ko ta halin kaka.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Click to subscribe my channel