Facebook na sauarara hirar mutane ta waya

0 5

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kwararru na cewa kamfanin shafin sadarwa
na Facebook yana sauraron hirar da mutane
keyi ta kan wayarsu a koda yaushe.
Kafanin na samun damar yin haka ne ta
hanyar amfani da app din Facebook dake cikin
wayoyin
mutane, inda yake tattara bayanai da sauraron
duk abinda suke cewa.
Sai dai a nashi bangaren Facebook ya amince
cewar tabbas yana tattara bayanan sauti daga mutanen dake amfani da app din sa, kuma ba wai yana yin hakan bane domin samun bayanai kan mutane wajen sanin abin da zai tallata musu
ba. yana yin hakane domin neman hanyar da zai bunkasa app din sa don moriyar mutane.
Wannan abu dai ba sabon abu bane tun shekarun baya aka gano kamfanin na yin haka, abin da ya
ja hankalin mutane a baya bayan nan shine lokacin da Farfesa Kelli Burn, na Jami’ar Jihar
Florida ya gargadi mutane kan wannan lamari.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.