EFCC Ta kama Matasa 6 Saboda Damfara A yanar Gizo

0 549

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Tu’annati (EFCC), ta samu nasarar kama wadansu matasa 6  da ake zargi da yin damafar ta Intanet da ake ira ’yan yahoo-yahoo. Ana zargin matasan ne da aikata damafara ta miliyoyin Naira daga hannun mutane a ciki da wajen Najeriya ta hanyar amfani da Internet.

A safiyar Talatar da ta gabata ce Hukumar EFCC ta kai samame a maboyar matasan da ke Rukunin Gidaje na Kolapo Ishola a kauyen Akobo kusa na birnin Ibadan  inda ta yi musu dirar mikiya ta kai ga kama  matasan wadanda aka same su da kananan motocin alfarma guda biyar da kwamfutoci da wayoyin salula da takardun bogi da aka tsara shirin damfarar mutane da su.

KARANTA WADANNAN;
1 of 94

Samamen ya biyo bayan yawan kararrakin da mazauna kauyen na Akobo suka rika shigarwa ne a baya game da hada-hadar  matasan da kai kawonsu tare da haramtattun ayyuka da suke yi wadanda al’ummar da ke zaune a wurin suka kyamaci irin sababbin miyagun ayyuka da matasan ke yi, inji majiyar Hukumar EFCC.

Matasan da aka kama masu shekara 24 zuwa 30 sun hada da Tella Adefemi da Ibrahim da Awoniyi Adeseye Abiodun da Oladele Olawale Wasiu da Olabiti Afeez Ajibola da Akeredelu Oluwafemi Temidayo da Oyaremi Olalekan Olabode, ana zarginsu ne da aikata miyagun ayyuka da suka hada da karbar miliyoyon kudi daga hannun mutane ta hanyar damfara ta  Intanet.

Majiyarmu ta ce da zarar Hukumar EFCC ta kammala bincike za ta gurfanar da matasan a gaban kotu saboda a yanke musu hukunci.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram