Efcc ta fara Gudanar Da binciken Bidiyon Karbar Daloli

0

Shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa sun fara gudanar da binciken zargin karbar rashawa da ake yi ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kamar yadda aka nuna a cikin wani bidiyo.

Magu ya bayyana haka ne a yayin dayake amsa tambayoyi bayan ya gabatar da wata kasida mai taken ‘Yaki da rashawa: mafita ga cigaban tattalin arzikin Afirka’ a jami’ar Queen Maru dake birnin Landan a ranar Juma’a 23 ga watan Nuwamba.

Majiyar Arewaclass.com ta ruwaito wani dalibin digirin digirgir, kuma lauya, Audu Bulama Bukarti ne ya nemi Magu yayi musu karin haske game da kokarin da yakeyi akan bidiyon Ganduhe, inda yace sun fara binciken, yana daga cikin abinda ya kais hi Landan ma.

KARANTA WADANNAN;
1 of 93

“Ya shugaban EFCC, wata jarida ta ruwaito kace ba zaku iya binciken Ganduje ba saboda dalilai guda biyu, na farko shine saboda gwamna ne mai ci, na biyu kuma shine saboda zai zama kamar cin dunduniyar shari’a

Amma ka binciki Fayose yana gwamna, haka zalika akwai wata hukunci da kotun koli ta Najeriya ta gabatar akan babban sufetan Yansandan Najeriya a shekarar 2002, inda tace za’a iya bincikar gwamnan dake kan mulki.

Sassaucin da tayi kawai shine ba za’a iya kamashi ko gurfanar dashi gaban kotu ba.” Inji shi.

Nan da nan Magu ya katse Bulama, inda yace basa gudanar da bincke ko wani iri a shafukan jaridu.

“Bidiyon nan na daga cikin dalilan da suka kawoni Landan, muna gudanar da binciken kwakwaf akansu, bana bukatar gudanar da bincikena a shafukan jaridu.” Inji shi.

#legithausa