Dole a hana Buhari ciyo bashin 5.5

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan takarar zama sakataren jam’iyyar PDP a zabenta na cikin gida mai gabatowa, Barista Mohammed Kabir Usman, ya bukaci ‘yan majalisar Najeriya da suyi watsi da bukatar shugaba Buhari ta ranto Dala biliyan 5.5.

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja, yana mai bayyana cewar ciyo bashin daidai yake da sayar da rayuwar matasan Najeriya masu tasowa.

Dalilan da yasa dole majalisa ta dakatar da Buhari daga ciwo bashin dala 5.5 – PDP Usman ya cigaba da cewar tattalin arzikin Najeriya ya fuskanci koma baya mafi muni tun shekarar 1999 a karkashin mulkin jam’iyyar PDP.

“Barin gwamnati ta ranto adadin
wadannan kudade daidai yake da cilla Najeriya cikin rigimar tattalin arziki na shekara 40, lokacin da Buhari ba lallai yana raye ba “. Inji Usman.

Sannan ya kara da cewar gwamnatin APC ta kashe bangaren masana’antu masu zaman kansu, dalilin da ya kawo rasa ayyuka da dama.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Hakazalika ya zargi gwamnatin APC da rashin fuskantar yadda harkokin tattalin arziki ke sauyawa lokaci zuwa lokaci.

A saboda haka ya ce bai kamata majalisa ta bari gwamnatin ta APC ta salwantar da rayuwar ‘yan Najeriya ba ta hanyar ciyo masu bashin da zai zame masu alakakai.

Usman ya ce hatta bangaren tsaro ya samu koma baya karkashin mulkin jam’iyyar APC. Ya bayyana cewar rikicin Fulani makiyaya ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu Dimbin yawa tare da yin kira ga sifeto Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris, da ya saki alkaluman ayyukan ta’addanci na shekara biyun mulkin APC domin kwatantawa da yadda harkar tsaro take karkashin mulkin jam’iyyar PDP.

©naijhausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.