[Doka]Dole kowa yayi gwajin HIV kafin aure a Jihar jigawa

0 3

Click to subscribe my channel

Gwamnatin jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ta rattaba hanun kan wata doka da ta wajabta yin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki ga duk mutanen da suke shirin yin aure a jihar.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin rage yaduwar cutar ta HIV a jihar bayan gano cewa ana saurin yada cutar tsakanin ma’aurata.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Mataimakin gwamnan jihar Barister Ibrahim Hassan Hadejia ya shaidawa BBC cewa an samar da wuraren yin gwajin kyauta a sassa dabam dabam
na jihar.

Dokar ta tanadi hukunci ga duk wanda ya nuna kyamata wajen yin gwajin kafin yin aure da kuma
hana tsangama ga wadanda aka samu suna dauke da cutar.

Click to subscribe my channel