Dembele zai koma Liverpool a Matsayin Aro

0 14

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ousmane Dembele yanason barin kungiyar domin komawa Liberpool a matsayin aro a kaka mai zuwa bayan da dan wasan bai samu buga wasanni da yawa ba a kungiyar.

Dembele, mai shekara 21 a duniya yakoma Barcelona
ne domin ya maye gurbin Neymar wanda yakoma PSG a
kakar wasan data gabata sai dai tun bayan komawarsa
kungiyar ta Barcelona yake fama da matsaloli.

Dan wasan dai yayi fama da rauni wanda yasa yayi kusan watanni hudu batare daya buga wasa ba a kungiyar kuma bayan yadawo duk da haka bai samu wasanni da yawa ba sannan kuma bugu da kari
kungiyar ta Barcelona ta siyo Coutinho daga Liberpool.

Kungiyar kwallon kafata Liberpool dai tana zaracin dan
wasan Dembele sai dai Barcelona bazata siyar da dan
wasan ba saboda tana ganin nan gaba zai iya haskawa
sakamakon karancin shekarunsa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 95

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool dai tana son dan
wasan amma a matsayin aro yayinda Barcelona takeson
duk wanda zai dauki aron dan wasan sai ya biya wasu
kudade.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ma tana zawarcin
dan wasan domin yakoma kungiyar a matsayin aro
amma kuma bazata iya biyan adadin kudin da Barcelona take bukata ba domin daukar dan wasan aro.

Barcelona dai ta biya fam miliyan97 wajen siyan dan
wasa Dembele daga kungiyar Borussia Dortmund kuma
tun bayan komawarsa kungiyar wasanni 23 kawai ya buga a kungiyar a dukkan wasannin kungiyar.

#leadershipayau

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram