Dangote ya bada tallafi

0

Gidauniyar Dangote, mallakar hamshakin mai kudin nan, Alhaji Aliko Dangote ta kaddamar da
fara raba kayayyakin abincin tallafi na Ramadan ga ‘yan gudun hijira a Borno.

Mutane dubu 371 ne ake tsammin za su ci moriyar raba abincin a cikin kwanaki 40 masu zuwa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Da yake bude taron, gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima ya yaba a yunkurin Dangote, inda ya ce tallafin da gidauniyar sa ke bayar wa na matukar tallafawa mutanen jahr Borno a cikin halin da suka tsinci kan su.

Kayan abincin wadanda aka isar a cikin tireloli dai sun kunshi abubuwa guda 10 kamar haka:
Shinkafa, alkama, Semolina, Maggi, Wake, Indomie, gishiri, Sikari, Taliya, da tumatir.