Dan sanda ya nemi chanjin wajen Aiki Saboda Maryam Yahaya

0 190

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Labari da muke samu ya nuna cewa wani jami’in dan sanda mai sune Rilwani Bala yace ya nemi sauyin wajen aiki daga jihar Sokoto zuwa Kano.

A cewar jami’in ya nemi wannan chanji na wajen aiki ne domin kawai ya dunga ganin sahibar ransa Maryam Yahaya.

Maryam Yahaya dai wata sabuwar jaruma ce a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wacce a yanzu tauraronta ke kan haskawa, kasancewarta mai karancin shekaru da kuma tarin kyau. An tattaro inda jami’in tsaron ke cewa

KARANTA WADANNAN;
1 of 127

“Ina Son Na zama Daya Daga Cikin Cikakkin Masoyin Maryam Yahaya Shi Yasa Na Shirya Tsaf Domin Neman Transfer Zuwa Kano Da Aiki Saboda Na Dinga Ganinta.

“Kuma Ina Yi Mata Fatan Zama Jaruma Mafi Daukaka A Duniyar Fina Finai Hausa. Kuma Da Duk Nayi Sallah addu’ata Kenan”.

Shafin kannywoodcelebrities ce dai ta wallafa wannan labara a shafinta na Instagram.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram