Dan NEPA yasha duka har da karyawa a gun dan sanda

0 2

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Wani ma’aikacin kamfanin wutan lantarki, na EKo, Dele Ogundele ya gamu da fushin wasu jami’an Yansanda bayan ya yanke wutan gidan mai gidansu, tsohon babban sufeton Yansanda, Mohammed Abubakar.

Jaridar Punch ta ruwaito dansanda mai suna Attah Aninoka ya wurgo jami’in NEPAn ne daga kan falwaya, sa’annan ya lakada masa dan banzan duka a ranar Alhamis 19 ga watan Oktoba, wanda yayi sanadiyyar karya masa kafa.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Dansandan yana fadin babu abinda zai faru, amma sai ga shi bayan da aka kai kararsa ga ofishin Yansanda, an kama shi, an daure shi.

Mutumin Shugaban hukumar rarraba wutan lantarki na Eko, Godwin Idemudia ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka an kama Dansandan, inda ya kara da cewa a yanzu haka ana bin tsohon Dansandan bashi N154,693.85.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Godwin ya bada labarin yadda lamarin ya faru kamar haka: “A ranar Alhamis da misalin karfe 12 na rana muka isa gidan, sai wani mutumi ya fito daga gidan muka tambaye shi ko sun biya kudin wuta, amma yace a’a, sai muka yanke musu wutan

“Wannan ne ya harzuka mutumin, sai dansandan ya fito, inda ya janyo jami’in namu daga kan falwaya, inda ya dinga dukansa, har ya ji masa ciwo tare da karya shi.”

Amma a nasu jawabin, Kaakakin Yansandan jihar Legas, ASP Olarinde Famous Cole ya karyata batun karya ma’aikacin NEPA.

©naijhausa

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram