Dalilin Kirkiro Shirin Tallafawa Matalauta da Shugaba Buhari Yayi

0 0

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Mataimaki na musamman ga mataimakin Shugaba Buhari, Alhaji Hafisu Ibrahim ya bayyana abun da ya sa gwamnatin Buharinta kirkiro da shirin tallafawa wadanda suka fi talauci a kasar.

Tallafin da aka kirkiro zai dinga ba wadanda suke cin gajiyar shirin Nera dubu biyar kowane baringwata.

Yace bisa da yin la’akari da irin halin
da wadanda suka fi kowa talauci a
kasar ya sa shugaban kasa ya fito da shirin tallafawa domin rage masu
radadin kuncin rayuwa.

Yace wanda ya riga ya tsufa babu abun da zai iya yi idan ba’a taimaka masa ba.

Dangane da inda aka samo kudin
tallafin Alhaji Ibrahim yace a cikin
kasafin kudin shekarar da ta gabata annyi tanadin nera biliyan dari biyar na tallafin.

Tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya Dr. Obadiah Mailafiya yace shirin ya zo daidai lokacin da ya dace amma akwai damuwa daya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Yace a sa ido a tabbatar wadanda ya kamata su samu kudin suka samu, kada a yadda da cin hanci ko yin cuwa-cuwa da kudin.

Amma acewar Sabo Gashuwa bada
tallafin ba shi ne mafita ba.

Yana ganin kamata yayi a sa kudin cikin abubuwan da zasu farfado da tattalin arziki.

Jihohin Bauchi da Neja na cikin jihohin da za’a fara dasu.

Misali a jihar Bauchi an fara shirin bada kudin ga mutane
10,800.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram