Costom na binkice akan jakunan da aka sato daga kasar kenya zuwa Nigeria

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kwastam na Bincike akan Fatocin Jakuna da aka Sato Daga Kasar Kenya Zuwa Nijeriya Jami’an sashen gudanarwa na hukumar kwastam ta Nijeriya (NCS) na neman wasu fatocin jakuna da aka sato daga kasar Kenya aka shigo da su Nijeriya ta jirgi. Gwamnatin Kenya dai ta dade ta na korafi akan yadda baki ke sace mata ma’adanunta, harda fatocin jakunan. Bayan da ta ji kishin kishin cewa wasu ‘yan cana guda biyu sun kawo wasu daga cikin fatocin Nijeriya kuma suna ajiye da su a ofishin ajiye kaya na hukumar kula da shiga da ficen kayayyaki ta jirgin sama na Nijeriya (NAHCON) da ofishin kamfanin Skyway aviation (SAHCOL), hukumar ta bayarda umarnin a rufe ofisoshin a ranar Litinin din da ta gabata. A jiya Laraba, jami’an hukumar sun kutsa kai ofisoshin ajiye kaya na kamfanonin biyu tun misalin karfe bakwai na safe domin su binciko fatocin, sai dai ba’a tabbatar sun samu abunda suka je nema ba. Kuma akwai jita jitan za su dawo gobe. Rahotanni na nuna cewa wasu ‘yan cana guda biyu ne suka shigo da fatocin Nijeriya daga kasar Kenya domin su yi amfani da kamfanoni Nijeriya wajen fitar da su zuwa kasar su. Har lokacin wannan rahoto, sashen fitar da kaya kasashen waje na ofisoshin biyu a kulle ya ke, sai dai an bar sashen shigowa da kaya a bude.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.