Cin hanci: Natanyahu zai fuskanci binciken ‘yansanda

0

Rahotanni daga kasar Isra’ila sun ce rundunar ‘yansandan kasar ta bukaci jami’an ofishin Farayin Minista Benjamin Natanyahu da su ware ma sa lokacin da zai je domin amsa tambayoyi kanbtuhumar yin almundahana.

Matakin ya zo ne kwana daya bayan da Atoni-janar na kasar Avichai Mandelblit ya amince da a yi wa farayin ministan binciken kwa-kwaf.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Tashar gidan Tallabiji ta Channel 10 da ke kasar tanIsra’ila ta ce yanzu haka ofishin farayin ministan na can na kokarin samun lokacin da ya yi wa Natanyahu daidai da ya je ya amsa tambayoyin.

Kafar watsa labaran ta ce manyan tuhumce-tuhumcen da ake yi wa Mr. Natanyahu su ne zamba-cikin-aminci da kuma karbar kyaututuka ba bisa ka’ida ba.