[Buhari]Mun duba kisan yan shi’a

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce za a dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka samu da aikata laifi a rikicin da ya faru tsakanin ‘yan shia da sojojin kasar a garin zaria cikin watan disambar bara. Wata sanarwa da mai taimakawa shugaban na Nigeiria kan kafafen yada labarai Garba Shehu ya futar, shugaba Buhari ya ce yana nazari kan rahoton da kwamitin bincike ya mikawa gwamnantin Kaduna kan rikicin. Ya ce masu fafutukar kare hakkin bil adama na gida da waje ‘su kwantar da hankalinsu’ domin kuwa duk wanda aka samu da laifi zai yabawa aya zakin ta. A lokacin wata tattaunawa da shugaba Buhari ya yi da manema labari a baya, shugaba Buhari ya ce ya na jiran rahoton kwamitin binciken, kafin ya dauki kowane irin mataki.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.