Buhari: Zamu gyara tsarin Yan sanda da Sharia idan muka Zarce

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari, yayi alkawarin gyara fannin yan sanda da shari’a don sakamako mai kyau akan yaki da rashawa matukar aka zabe shi a 16 ga watan Fabrairu.

A jiya da yayi jawabi ga magoya bayan shi a filin wasa na Abakaliki yayin zagayen kamfen a jihar, shugaban kasar yace gwamnatin shi tayi iyakar bakin kokarinta na cika alkawurran da tayi a 2015.

Yace APC zata cigaba da cika alkawurranta matukar aka kara zabarta don cigaba da mulki. Nasarorin mulkin shi sun hada da kwato wasu sassan jihar Borno da Boko Haram ta kwace tare da karbo yam matan Chibok da yan ta’addan suka sace.

“Babu wani bangare da yake karkashin Boko Haram yanzu. Sun sace tare da sanya mataye da samari muguwar hanya, ballantana yara mata masu kasa da shekaru 15.

Wadanda ake sakawa abubuwa masu fashewa a kuma turasu majami’u, masallatai, kasuwanni da tashar motoci.

A yanzu hakan yayi karanci,” inji shi.

KARANTA WADANNAN;
1 of 17

Shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa yaki da rashawa yana wahalar dashi a mulkin nashi.

“Amma muna iyakar bakin kokarin mu wajen ganin mun gyara bangaren yan sanda da shari’a.

Muna zabar mutane basu da komai amma cikin kankanin lokaci sai kaga sun mallaki gidaje da motoci tare da makudan kudade.

Muna kama su mu mika su ga kotu da fatan za a hukunta su,” yace.

A halin haka ne jam’iyyar PDP ta duba cigaban da aka samu da kuma tunanin zabe mai zuwa sai tace yakamata a kama gwamnatin shugaba Buharin da laifi akan shirin lalata zabe mai zuwa.

PDP tana cewa “Manjo Janar Babagana Mongunu, NSA yace “wasu mutane da suke tsoron sakamakon zabe mai zuwa na shirin yada hatsaniyar da zata lalata zabe mai zuwa.”
wata magana ta sakataren hulda da jama’a na PDP, Kola Ologbondiyan yace “Jam’iyyun siyasa da kuma yan takara takara da suke tunanin yanda sakamakon zabe mai mai zuwa zai kasance sune APC da kuma Dan takarar ta Muhammadu Buhari, Wanda ke nuna fushin shi akan kayen da za’ayi mishi.”

Kamar yanda jam’iyyar PDP ta fada, da yawan yan Najeriya sun kosa lokacin zabe yayi suje su zabi sababbin shuwagabanni da zasu fitar dasu daga yunwa, durkushewar tattalin arziki da kuma kuma kashe kashe.

A don haka ne APC ke da niyyar bata zabe mai zuwa, inji jam’iyyar adawan.

#legit.ng

Get real time updates directly on you device, subscribe now.