Buhari zai jagoranci tattaunwa a kan Gambia

0 0

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin wasu shugabanni 4 na kasashen yammacin Afrika domin tattaunawa kan dambarwar siyasar kasar Gambia, a ranar Litinin din nan.

Wata sanarwa daga fadar shugaban, ta ce, taron, ci gaban wata ganawa ce da shugabannin yammacin Afrikar suka yi a Accran Ghana, a
lokacin rantsar da sabon shugaban kasar, Nana Akuffo-Addo a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce shugaban zai jagoranci zaman ne domin lalubo hanyar da za a cimma masalaha a
dambarwar da ta biyo bayan zaben Gambian.

Ce-ce-ku-cen ya samo asali ne dai bayan da Shugaba Yahya Jammeh, wanda da farko ya amsa shan kaye a zaben, ya dawo ya ce bai amince da faduwar ba.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Shugaban ya zargi kasashen waje da cewa su ne suka rikita zaben, abin da ya sa ya ce ya gabatar da korafinsa gaban kotun kolin kasar.

Shi kuwa a nasa bangaren jagoran ‘yan hamayya Adama Baro, wanda aka ayyana ya ci zaben, ya lashi takobi cewa da zarar ranar 19 ga watan Janairu ta zo, zai tabbata shugaban kasar.

®bbc

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram