Buhari ya yi kira ga ‘yan Shi’a su zauna lafiya

0 2

Click to subscribe my channel

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘ya’yan kungiyar ‘yan uwa Musulmi wadanda aka fi
sani da ‘yan Shi’a da su rungumi turbar zaman lafiya.

Shugaban ya bayyana haka ne a sakonsa na sabuwar shekara.

Shugaba Buhari ya ce, “A matsayinsu na ‘yan uwanmu, muna kira ga ‘yan Shi’a su rungumi turbar zaman lafiya.

Dole su bi dokokin kasar da
suke zaune a ciki”.

Ya kara da cewa, “A lokaci guda kuma, dole jami’an tsaro su rika mu’amala da su ta hanyoyin
da suka dace da kuma bin doka kan yadda suke tunkararsu”..

Hakan na zuwa ne dai a yayin da ‘yan Shi’a ke ci gaba da korafi kan zargin gallazawar da jami’an
tsaron kasar ke yi musu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Hukumomin kare hakkin dan adam irin su Amnesty International sun ce jami’an tsaron na Najeriya sun kashe daruruwan ‘yan Shi’a a lokacin da suka bude musu wuta a birnin Zaria a watan Disambar shekarar 2015.

Bayan haka ne suka kama shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da wasu
manya-manyan ‘yan kungiyar inda har yanzu suke ci gaba da tsare su duk da hukuncin da kotu ta
yanke na sakin su.

‘Zaman lafiya a Naija Delta’
Shugaba Buhari ya kuma ce zai ci gaba da neman zaman lafiya da mazauna yankin Naija Delta mai
arzikin man fetur.

A cewarsa, “ina jaddada kira ga ‘yan uwana na yankin Naija Delta wadanda suke tayar da kayar-
baya da kuma yin zagon-kasa ga tattalin arzikin kasa da su zo mu sasanta.”

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce za su tunkari duk wani mutum da ba ya kaunar zaman lafiya, yana mai shan alwashin cewa ba zai bar wani ko wata su durkusar da Najeriya ba.

©bbc

Click to subscribe my channel