Buhari ya musalta zargin Albashi biyu

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba ya musalta wasu bayanai da ke zagaye a kafafan sada zumunta na cewar ya na karbar albashi har biyu daga asusun gwamnatin tarayya, daya na kasancewarsa shugaban kasa mai ci, daya kuma alawus din da ake baiwa tsoffin shugabannin mulkin soja. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasan, Garba Shehu ya fitar a shafin sada zumunta na Twitter, ya bayyana cewa tun da shugaban kasar ya hau kan mukaminsa na yanzu a watan Mayun bara, sisi bai karba ba daga bangaren sojojin ba a sunan alawus. Ya ce ko fanshon sa a matsayinsa na tsohon soja ba ya karba, ba kamar sauran ‘yan uwansa ba. Ya kuma ce tun lokacin da aka yi masa juyin mulki, sojojin basu taba samar masa wani tsari na biyansa fansho ba. Haka kuma sanarwa ta ce, shugaban kasar bai taba karbar gratuti ko motoci ba kamar yadda tsoffin shugabannin mulkin sojan ke karba, ya kara da cewa bayan da aka yi masa juyin mulki, ba’a tunawa da shi ko a wajen raba kalandu da littatafan sojojin. A karshe sanarwar ta ce za’a iya tantance wadannan batutuwa a ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.