Buhari ya magantu akan tsadar man fetur

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna
jimaminsa dangane da wahalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta na karanci man fetur.

“Ina jajanta wa dukkan ‘yan Najeriya game da wahalar rashin man fetur da kuma yadda suke jure wa wahalhalun bin dogayen layuka domin neman man,” inji shugaban a cikin wani jawabi da BBC ta samu.

“Ana sanar da da ni halin da ake ciki
musamman irin kokarin da kamfanin mai na kasa, NNPC ke yi domin samar da isasshen man fetur a wannan lokacin da kuma nan gaba.”

Shugaban ya kara da cewa “Kamfanin na
NNPC ya tabbatar min cewa za a sami saukin yanayin a cikin kwanaki masu zuwa.”

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ya sanar da ‘yan Najeriya cewa ana sa ran shigowar man fetur daga lkasashen waje, kuma za a raba man zuwa dukkan sassa na kasar.

Shugaban ya kuma ce ya umarci hukumomin da lamarin ya shafa da su “dada kaimi wajen dakile masu boyar da man fetur da kuma ‘yan kasuwa masu kara kudin man.”

©bbc