Buhari ya kori babbachir ya maye gurbin sa Da Boss Mustapha

0 2

Click to subscribe my channel

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sawwake ma babban Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal, inda ya maye gurbinsa da Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya.

Har ila yau shugaba Buhari ya dakatar da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA, Ambassador Ayo Oke.

Wata sanarwa da mai ba shugaban
shawara kan yada labarai Femi Adesina ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarwarin da kwamitin da
ya binciki manyan jami’an gwamnatin biyu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Dukkan mutanen biyu dai sun musanta zarge-zargen.

Shugaba Buhari ya kuma amince da
kafa wani kwamitin musamman mai
mambobi uku don yin nazari akan
ayyukan hukumar NIA.

Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai bada shawarwarin yadda za’a inganta ayyukan hukumar tattara bayanan sirrin ta NIA.

©naijhausa

Click to subscribe my channel