Buhari Ya Cika Dukkanin Alkawuran Da ya Dauka-Lai Mohammed

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ministan sadarwa da al’adu, Lai Mohammed ya ce, Shugaba Buhari ya cika dukkanin alkawurran da ya dauka a zamanin yakin neman zabensa, don haka ya cancanci a sake zaben sa a karo na biyu.

Ministan ya fadi hakan ne a Abuja, ranar Talata lokacin da ya bayyana a cikin wani shiri na kamfanin dillancin labarai na kasa mai taken, Dandalin NAN.

Ministan ya ce, tun lokacin da gwamnatin Shugaba Buhari ta hau karagar mulki ta yi alkawarin magance matsalar tsaro, yaki da cin hanci da karban rashawa da farfado da tattalin arzikin kasa.

“Mutane da yawa sun yi zaton ba zamu iya yin bikin kaddamarwa a dandalin Eagle Skuare ba, saboda har lokacin da muka kafa gwamnati a yashe wurin yake na tsawon shekaru ba a amfani da shi.

“A lokacin da aka rantsa da Shugaba Buhari, kananan hukumomi 20 daga cikin 27 na Jihar Borno, gami ma da wasu guda hudu a Jihar Adamawa, duk suna karkashin ‘yan Boko Haram ne.

“Shekaru uku da rabi bayan nan, zan iya bugun kirji na fada ba tare da shakkan kowa ba, ko inci daya na kasar nan ba shi a karkashin Boko Haram din.

Ya ce, bai kamata a kalli nasarar da gwamnatin tarayya ta samu a kan yaki da cin hanci a bisa yawan mutanan da aka kama, aka yi masu hukunci ko aka daure su ba.

Kamata ya yi a kalli abin ta fuskacin irin tsare-tsaren da aka yi na tabbatar da ana yin komai a cikin gwamnatin nan a fili, ta hanyar aiwatar da asusun bai-daya.

A cewar shi, “Ba mu muka kirkiro asusun bai-daya din ba, amma da muka zo mun taras ana tafiyar da shi ne a hargitse, inda gwamnati take da asusun ajiya a Bankuna sama da, 22000.

“A tsakanin 2015 zuwa yau, Naira triliyon 8.9 sun shiga asusun na bai-daya, hakan ya sa gwamnati tana sanin ko nawa ne take da shi a kowane lokaci, ta kuma san abin da ya kamata ta yi da shi.

Ya ce, ta hanyar bullo da shirin nan na masu fasa kwai, ya sanya gwamnati ta iya kwato Naira bilyan 13.8 na wadanda suka ki biyan haraji, da kuma wani karin na Naira bilyan 7.8, dala milyan 378 da Fam 27,200.

Ministan ya ce, kudaden da ake samu daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban ya karu sosai tun hawan wannan gwamnatin.

Ya ce, tattalin arziki ya habaka sosai, ta hanyar samar da shirye-shiryen tallafawa kamar na N-power, musayar kudi da ciyar da yaran makaranta abinci.

“A karkashin shirin na N-power an samar wa da sama da matasa 500,000, wadanda suka kammala karatun digirin din su ayyukan yi, a kan shirin bayar da tallafin kudi kuwa, mun baiwa matalauta 297,000, Naira dubu biyar-biyar

Get real time updates directly on you device, subscribe now.