Bercelona ta dauki spanish super cup

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Barcelona ta dauki Spanish Super Cup bayan da ta doke Sevilla da ci 3-0 a karawar da suka yi a Camp Nou ranar Laraba a wasa na biyu. A wasan farko da suka buga a ranar Lahadi Barcelona ce ta ci 2-0, jumulla ta doke Sevilla gida da waje 5-0. Wannan shi ne karon farko da Barcelona ta ci Spanish Super Cup tun wanda ta dauka a 2013. Hakan kuma na naufin za a fara gasar La Liga ta bana a ranar Juma’a, a ranar Asabar Barcelona za ta kece raini da Real Betis a gida. Ita kuwa Sevilla za ta karbi bakuncin Espanyol ce.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.