Bazan Auri namiji saboda kyaunsa ba sai dai saboda wasu abubuwa kamar:

0 38

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Rayuwar soyayya akwai dadi kuma yana yin ta yana saka masoya cikin nishadi da mararin juna, ta wani fuskar kuma takan saka kunci da kuma damuwa idan har akayi rashin dace, ba kowanne masoya ne soyayyarsu take kai su da aure ba, ma fi akasari an fi samun masoyan da suka tafka soyayya da juna ba tare
da sun auri junan nasu ba,walau a karshe su rabu
saboda wani dalili na daban wanda ya gifta ta tsakiyar
soyayyarsu ko kuma dayan ciki ya rasu.

A bisa bincike
irin na masana soyayya sun gano faruwar hakan dai-
daiku ne suke iya auran junansu ko da kuwa sun auri
junan nasu soyayyar wasu ba ta karko dan ba a iya
karshen ta a gidan aure nan gaba kadan zan yi bayani
game da wannan matsala ta masoya. Da yawan lokaci
wannan shafi yakan karbi bakin masoya daban-daban
don jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rayuwar
soyayyar su don sauran masoya su ji su kuma kara
kyautata soyayyar su wanda yake na gyara, su gyara.

A yau ma wakiliyar wannan shafi Muhiebert Abdullahi ta
karbi bakuncin hadaddiyar masoyiya ga kuma yadda
tattaunawar ta kasance:

Barkanki da kasance wa cikin wannan shafi na soyayya
da shakuwa Yauwa barka dai.

Da farko za mu so mu ji cikakken sunanki da kuma
sunan da aka fi saninki da shi da kuma dan takaitaccen tarihinki.

Sunana shi ne Fateema Muhammad Argungu amma an fi sani na da Zarah Bint Muhammad, Shekaru ta 22 ni
haifaffiyar garin birnin Kebbi ce a nan na yi firamare da sakandire dina, bayan na kammala na samu admission a jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato inda nake karanta Pure Islam a mataki na 3(300 lebel) Masha Allah!

Shin malama Fatima kin taba soyayya ko kuwa tukunna dai?

Ehh na taba but not that serious irin sama-sama haka.

Me ya ja hankalinki har kika fara soayya?

Gaskiya ba zan iya cewa ga abin da ya ja hankalina
wajen fara soyayya ba, kawai na tsinci ni da fara ta.

Za ki kamar shekara nawa kina soyayya, kuma kina kamar shekara nawa kika fara soyayya?

Gaba daya ba a shekara biyu ba, kasancewa ta a ciki
har ma da fara ta din.

Shin a cikin shekara biyun da ki kai da fara soyayya kin taba samun wani kalubale ciki?

Ehh a gaskiya na taba samun kalubale Ko za ki iya fada mana irin kalubalen da kika taba fuskanta?

Kalubalen da na samu shi ne genotype dinmu, combination din bai yi daidai ba, saboda dukkan mu mun kasance carrier.

Baya ga haka ba ki taba samun wani kalubale ba?

Ehh akwai wani but wannan family issue ne Bayan da kuka gano ku carrier ne kun ci gaba da soyayyar ne ko kuwa rabuwa kuka yi?

A’ah Ba ma tare rabuwa muka yi.

Wacce hanya kuka bi wajen rabuwa da junanku musamman yadda kuka sha soyayya?

Ta hanyar tawakkali ga Allah, yarda da kaddara saboda
haka Allah ya tsara Kuma shi ne ma fi alkairi a rayuwarmu.

Ya batun yaudara da ake ta yawan maganarta shin an
taba yaudararki?

KARANTA WADANNAN;
1 of 5

A’ah ba a taba yaudara ta ba.

Ko za ki iya yi mana bayani yanda yaudara take a
takaice?

Toh yaudara ma kashi-kashi ce, yaudara wata hanya ce wanda namiji ko mace kan iya bi wajen cutar da junansu ta hanyar soyayyar karya da makamantan haka.

Gaskiya ne! Idan kika ci karo da wanda ya yaudare ki
shin wanne mataki za ki dauka?

Ehh toh idan har Allah ya jarrabe ni da mayaudari, toh
matakin da zan dauka shi ne hakuri saboda shi ne maganin komai a rayuwa, idan ka bar wa Allah komai shi ne zai ma ka magani Kuma yai maka zabi ma fi alheri.

Masha’Allah! kasancewar muna cikin watan Ramadan ya kike gudanar da soyayyarki misali kamar wajen ba wa junanku kula wa zuwa zance ko makamancin hakan?

Ehh toh Ba na soyayya a yanzu gaskiya Ke nan tun bayan rabuwarku da wancen baki kara ci gaba da soyayya ba?

Ehh

Me ya hanaki soyayya a yanzu ko kuwa zafin rabuwa
da shi ne ya janyo daina soyayyarki duk da kin ce
soyayyar da ki kai ba tai tsanani ba?

A’ah ba zafin rabuwa ba ne gaskiya saboda can baya
na fada I am not addicted, kawai na zauna abina ne
haka nan.

Hakane! Idan na fuskance ki gaba daya rayuwar soyayyar ta ki da mutum daya kika yi ta haka ne?

Ehh haka ne.

Yanzu kuma ba ku tare saboda wasu dalilai shin yaushe kike tunanin za ki ci gaba da yin soyayya?

Ni kaina ba zan ce miki ga lokacin ba, Allah kadai ya
san ko wanne lakaci ne.

Gaskiya ne, wanne irin farin ciki kika taba fuskanta
cikin soyayya?

Toh Alhamdu Lillah na samu farin ciki ta yanda nake samun kulawa daga wajen shi
Masha’Allah! Wasu masoyan sukan kira soyayya da
munanan kalmomi kamar soyayya masifa ko bala’i da
dai sauransu ya zaki kwatanta yanda soyayya take a
wajenki?

Ehh it’s defends da irin wanda kuke tare duk wanda kika ga ya kira soyayya da mummunan kalma to yana da dalili, haka ma wanda ya yaba to Shi ma yana da nasa dalili,but gaskiya ni am not addicted da ita.

Wasu Mazan idan suka ga mace a hanya suka ji suna santa sukan yi kokarin ganin sun tsaida ita domin sanar mata da abin da yake zuciyarsu, shin idan hakanbya faru a kanki za ki tsaya?

kuma ya za ki dauki
soyayyar ta sa a lokacin?
A’ah ba zan iya tsaya wa ba.

Ba na ganin ya dace namiji ya tare ni a hanya cewar yana sona, ban son irin wannan halayya kuma idan ma hakan ta faru gaskiya ba zan ba shi kulawa ba duk da cewa wani lokacin babu
yanda za su yi wannan ita ce damar da suka samu,
kuma idan ta wuce shike nan may be ba za su kara
gani na ba.
Hakane! toh wanne irin namiji kike son aura?
A rayuwa ta ina burin auren namiji wanda ya kasance
well educated both Islam da na boko haka wanda ya
san darajar mace da ta iyayenta,haka ya san darajar
addininsa.
Wanne irin namiji ne kuma ba ki so ?
Ban san namijin da bai wadatu da ilimi ba both na
Arabia da na zama sannan wanda bai sani darajar
dan’adam ba, saboda irin wadannan ko darajar aure ba
za su sani ba.
Ya batun kyau fa? Wasu matan ma fi akasari sukan ce
sun fi son namiji kyakkyawa, fari wanda kamar shi ya
yi kansa, mai kudi da dai sauransu, shin ya hakan yake
a wajenki?
Ba na duba da wannan, saboda ba kyan ne zai min
zaman aure ba, kyan halayyar sa shi ne zai sa aure ya
dore.
Haka ne! Ya batun kishiya fa? Shin kina cikin matan
da suke son a yi musu kishiya ko kuwa ya abin yake?
Toh auren fiye da mata daya dama ce wacce maza
suka samu daga Allah(SWT) fargaba ta ita ce ban san
wacce zan tarar ko wacce za ta tarar da ni ba,fatana
idan har ina da rabon zama da kishiya Allah ya datar
da ni da ta kirki.
Da kyau! Na kan ji wasu ‘yan matan na addu’ar cewa
Allah ya ba su namijin da iyayensa suka rasu saboda
tsoron tashin hankalin uwar miji da ake yawan fada,
shin ya hakan yake a wajenki?
A ganina wannan bacewar basira ce, kuma ba haka
yake a wajena ba
Da kyau! Wanne irin jan hankali za ki ga masu irin
wannan tunanin?
Toh Jan hankali ga mata masu irin wannan tunanin shi
ne rayuwar iyayen mijin da rashin ta ba shi ne jin
dadin aure ba,wani sa’in ba sa raye amma kuma ba
kajin dadin mijin, idan har za ki jajirce ki zama suruka
ta kirki sannan kina haduwa da addu’a saboda shi
zaman aure sai an hada da addu’a, idan kina hakan
insha’Allah ba za ki samu matsala ba, idan ma Kin ga
matsala still bayan kina kokari to jarabawa ce daga
Allah Kuma idan ki ka yi hakuri za ki ci riba gaba.
Da kyau! Idan muka duba yana yin soyayyar yanzu ta fi
karkatuwa ne ga social media ya za ki kwatanta
soyayyar zahiri da kuma ta soyayyar network a
wajenki?
Toh ni a gani na soyayya wacce a kan network kawai
ta ta’allaka Kamar bata lakaci ne, sai dai ana iya
haduwa a social media har ta kai ga aure but ace
haduwar media a yi soyayya a rabu Kuma duk a media
duk shirme ne a gani na soyayyar zahiri ta fi tasiri
sosai gaskiya.
Idan kika ci karo da wanda ya ce yana sonki a social
media za ki iya yarda da soyayyar da yake miki har ki
amince?
Ya danganta da yanda ya tunkare ni da maganar,wani
namiji na da hikima wajen iya magana har mace ta
aminta da shi wani Kuma magana daya zai yi in ji
cewa wannan ban san abin da yake ba.
Wanne irin kalar abinci kika fi so?
Ban da abincin da na fi so, kowanne ya samu
Alhamdulillah
Da kyau! kayan sa wa fa wanne iri kika fi so?
A fanni tufafi na fi son atamfa
Wanne kala ne ya fi burge ki a rayuwarki?
Ash and gold.
Wanne suna kika fi so masoyinki ya kira ki da shi?
Duk Wanda ya burge shi ya kirani da shi
Da kyau! Wanne shawara za ki ba wa masoya?
Shawara ga masoya ita ce a duk lokacin da zama ya
hadaka/ki da masoyi, a yi soyayya don Allah kuma kada
a ci amanar juna, sannan dole sai an hada da hakuri
sannan za a cim ma burin da ake son akai.
Malama Fatima Zarah muna godiya da fatan za ki sha
ruwa lafiya.
Ni ma na gode.
Wannan shi ne karshen tattaunawar da wakiliyar
wannan shafi ta yi da Fataima zarah ku kasance wani
makon da ganin da mai shafin zai tawo muku da shi,
Kusha Ruwa lafiya Masoy.

#pulse

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram