Bani da wata dangantaka da Buhari-Kwamishinyar Zabe

0

Kwamishinar ta hukumar zaben Nijeriya INEC Amina Zakari ta musanta cewa tana da dangantaka ta jini da shugaba kasar Muhammadu Buhari.

KARANTA WADANNAN;
1 of 104

Wasu ‘yan siyasar kasan ne dai suka fara zarge-zargen cewa tana da dangantaka da Buhari, don haka suna da shakku kan adalcin da INEC za ta yi a zaben dake tafe.

An nada Amina a matsayin mai kula da tattara sakamako, abinda ya sa ‘yan adawar ke ganin za a yi musu magudi.