Ban 24hours Aisha Wakili sojoji basu fara tambayar ta ba

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yanzu haka Aisha Wakil, lauya a Nijeriya kuma kuma mai shiga tsakanin kungiyar Boko Haram da gwamnatin Nijeriya wacce ta mika kanta ga rundunar sojin Nijeriya ta na nan a hannunsu ba’a fara mata wasu tambayoyi ba. Aisha wacce ta mika kanta tun jiya Litinin, kasa da awanni 24 bayan da rundunar ta sanarda cewa ta na neman ta, ta yi matukar mamakin ganin sanarwa a kafafaen yada labarai duba da yadda ta ke sananniya a cikin sojojin. Mai magana da yawun rundunar sojojin Sani Usman ya tabbatar da cewa Aisha tana hannun su kuma tana cikin walwala, sai dai har yau da rana ba’a shiga yi mata wasu tambayoyi ba. Rundunar sojin dai ta sanar da neman mutane uku da suka hada da ita Aisha Wakil din, da Ahmed Bolori da kuma dan jarida Ahmad Salkida a ranar Lahadin da ta gabata a kan zargin suna da wata alaka da kungiyar Boko Haram.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.