Babu wanda ya tsara daga satar bayanai a Twitter

0

Wata kungiyar masu kutse a yanar gizo dake kiran kansu da suna
OurMine, tace tana kaiwa fitattun kamfanoni hari a shafikansu na kafofin sadarwa domin ta tallata aikinta na tsaro.

Kungiyar OurMine dai ta kai wa shafukan kamfanoni da suka hada da babban kamfanin nan dake yin wasannin video game mai suna Marvel Hero da The Avengers da Captain America da kuma Ant-Man, hari inda suka kafe wani sako iri ‘daya a duk shafukan wanda ke cewa “Sannu, OurMine ne, karka damu muna gwajin tsaron ka ne, a tuntubemu mu taimaka maka wajen tsaro.”

Biyo bayan wannna sako da suke kafewa a duk shafin da suka yiwa kutse, suna kuma barin adireshinsu na email domin a tuntubesu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ita dai wannan kungiya dake ikirari da suna OurMine, akan shafinta na yanar gizo tana yin tallar bayar da tsaro ga shafukan yanar gizo da kuma shafukan dandalin sada zumunci musamman ga kamfanoni ko wasu fitattun mutane, akan farashin Dalar Amurka 30 ga shafukan sadarwa, ko shufukan yanar gizo na kamfanoni akan kudi da ya kai Dala dubu ‘daya zuwa Dala dubu biyar.

A farkon wannan shekara ne dai mujallarfasaha ta TechCrunch ta fitar da rahotan cewa wasu matasa uku ne suka kafa wannan kungiya, matasan da mujallar bata bayyana ko su waye ba.

cikin manyan sunayen da kungiyar
tayiwa kutse har da shugaban Facebook Mark Zuckerberg da shugaban Google Sundar Pichai.