Baba nane sillar zamana yar shaye shaye

0 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Binta (wadda ba sunanta na asali ba
ne) ta zauna a daki ita kadai.

Yanayin kunci da bakin cikin da take
ciki, ya sanya dakin ya yi tsananin
duhu fiye da ainihin duhun dakin.

Cikin shessheka da kokarin tsaida
hawayen da yake fita daga idanunta ta hanyar amfani da takardar goge hannu ta share fuskarta tare da daidaita muryarta don fara ba ni lanarin rayuwarta…Hawayen ba su tsaya ba, muryarta na rawa ta fara magana:

“Na rasa mahaifiyata lokacin da nake da kananan shekaru kuma tun daga lokacin ban taba samun kwanciyar hankali ba a rayuwata.”

Ta ci ga da cewa: “Mahaifina ya auri
wata matar wadda ta rika gasa mana ukuba da ni da sauran ‘yan uwana.

A da yana da damuwa da mu, amma
bayan da ya yi aure sai ya yi watsi da mu.”

“Daga nan ne sai na fara yawace-
yawace don neman hanyar da zan kula da kannena…a haka ne na hadu da wani mutum wanda ya yaudare ni.”

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

“Ya yaudare ni, ya yi min ciki. Kuma ya matsa min lamba cewa sai na zubar da cikin amma sai na ki.”

Binta ta ce mahaifinta ya goyi bayanta da farko, amma daga bisani sai ya “kore ta daga gidansu.”

Ko ya dace a yi gwajin cutar sikila
kafin aure?

“A wannan gabar ce na fara shaye-
shaye da kuma bin kawayen banza. Ba na kaunar irin wannan rayuwa.

So nake na koma makaranta don na zama lauya.”

Binta tana daya daga cikin dimbin
yaran da wadansu iyaye ke watsi da
su.

Wannan ne wani abu da ake yawan
samu a arewacin Najeriya, inda iyaye da dama suke nuna halin ko in kula da ukubar da ‘ya’yansu suke ciki.

©bbchausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.