Biyo bayan cece-kucen ne jarumi Adam Zango ya wallafa wani hoto na shugaba Buhari a shafinsa na instagram inda yake kara jaddada ma jama’a cewa har yanzu yana tare da shugaba Buhari dari bisa dari.

“A nan nake, kamar yadda na fada a baya, ba biya akayi nake goyon bayan Buhari ba. Ra’ayi na ne, wanda hakan bazai hanani yiwa dan PDP murna ba muddun ina da alaka da shi.” inji jarumi Adam Zango.

Akwai wasu daga cikin yan wasan kwaikwayon da tuntuni sun nuna goyon bayansu ga Alhaji Atiku Abubakar wanda wasu daga cikinsu ma akwai masu yi masa campaign. Daga ciki akwai irinsu Fati Muhammad da Kuma jarumi Al-amin Buhari.