APC bazata tsai da Buhari takara ba har sai tatabatar da wani abu

0

Kakakin majalissar Wakilai, Yakubu
Dogara yayi tsokaci akan kara tsayawa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dogara yayi yan jarida jawabin a
lokacin da ya fito daga taron majalissar zartarwa na jam’iyyar APC ranar Talata.

Dogara ya ce, jam’iyyar su za ta duba nasoroin da gwamnatin Buhari, da cika alkwaran da ta yi wa yan Najeriya kafin su fara tunanin kara tsayar da shi takara.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Dogara ya bayyana abun da zai faru kafin APC ta fara tunanin kara tsayar da Buhari takara Dogara ya ce “ba saboda zaben 2019 suka yi taro ba.

“Mun gudanar da taron ne dan duba
matsalolin da kasar ke fuskanta da
tunatar da junan mu alkwarran da muka yi wa yan Najeriya lokacin yaki neman zabe,

“kuma mun duba nasarori da kalubale da jam’iyyar ta ke fuskanta, da kuma hanyoyin da za mu bi dan gayara kuskure mu nan gaba.

©naijhausa