Ankama wani da jabun 880,000 dolar yacce aljannu ne suka aike shi

0 2

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

‘Yan sandan Jihar Neja sun yi ram da wani mai suna Abubakar Suleiman, dauke da jabun 880,000 na dalar Amurka

Suleiman ya ce shi dai dan aiken aljannu ne, bai san kudin jabu bane

Hukumar ‘yan sanda ta ce Suleiman na cikin kungiya masu yawo da kudin bogi wanda ta ke nema ruwa a jallo.

Abigail Unaeze, mai magana da yawun Hukumar ‘yan sandan Jihar Neja, ta ce ‘yan sanda sun yi ciki da wani Abubakar Suleiman yayin da ya kai wa wani Injiniya Abdullahi Sambo jabun 880,000 na dalar Amurka, a yankin Shango na garin Minna.

Wani dan uwan Sambo mai suna
Mamman Manya ne ya kai Suleiman
kara ofishin ‘yan sanda da ke
Chanchaga.

Suleiman dai ya amsa laifin
mallakar jabun kudi amma ya yi
ikirarin aljannu ne su ka umurce shi ya karbi kudin a hannun wani mai suna Khalifa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Aljannu ne su ka aike ni da kudin, in ji wani da ‘yan sanda su ka kama da jabun dalar Amurka Suleiman dai ya ce aljannun sun kira shi ne su ka umurce shi ya karbi sako daga hannun Khalifa, ya kai wa Sambo.

Ya ce kuma sun yi alkawarin zasu
taimake shi da kudi, amma baya ga
wanann bayani, bai san komai ba.

Suleiman ya kuma ce ya yi ta kiran
khalifa ta wayar tarho amma ya ki ya daga wayar ta sa. Ita kuwa Hukumar ‘yan sanda ta ce, Suleiman ya na cikin wata kungiyar masu yawo da kudaden boge ne wanda daman Hukumar ke neman su ruwa a jallo.

©hausa.naij.com

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram