Anayin halin ko in kulla ga ilimi a wannan gwamnati

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai
(MURIC), ta yi Allah wadai da kashi 7 da a ka ba wa fanin ilimi a kasafin 2018 daBuhari ya gabatar ma Majalisa.

Shugaban Kungiyar, Farfesa Ishaq
Akintola, shi ne ya bayyana hakan a
Ranar Laraba.

Kungiyar ta yi nuni da cewan
sakamakon halin ko-in-kula da wannan gwamnatin da gwamnatocin baya su ka yi ga harkar ilimi, ya sa harkar ta tabarbare.

Ya isa misali yadda kashi 70
na dalibai sun kasa cin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare na 2017/2018.

Haka dalibai ke fadi warwas ko wace shekara, in banda 2016 da a ka samu kashi 50 da su ka ci.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Shi ma din ba wani abun alfahari bane, in ji kungiyar.

Don kuwa Kungiyar Kula da Ilimi da
Kimiyya da Al’adu na Majalisar Dinkin Duniya, (UNESCO), ta shawarci ba wa ilimi kashi 26 na kasafi.

Ita kuwa Najeriya ko yaushe sai dai ta yi kunnen uwar shegu ga wannan
shawara, ba a taba samun kaso mai
tsoka ba, ballanta wanda ya kai kashi 26.

A cewar kungiyar, ta yaya kuwa
za’a samu cigaba a harkar ta ilimi?

Kungiyar ta kalubalanci Gwamnatin
Tarayya da ta yi gaggawan kawo gyara da kuma sanya takunkumi a lamarin, ta yadda za a hana jami’an gwamnati da ‘yan siyasa tura ‘ya’yan su kasashenwaje neman ilimi.

©naij

Get real time updates directly on you device, subscribe now.