Ana Kyautata Zaton ‘Yan Boko Haram Ke Kai Hari Jihar Neja

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Akwai alamun hare haren da ake kaiwa jihar Neja ‘yan Boko Haram da aka tarwatsa daga dajin Sambisa ne suke haddasasu tare da sace dabbobi da dukiyoyi Wasu mahara da kawo yanzu ba’a tantance ko su
wanene ba dauke da manyan bindigogi sun afkawa wasu kauyuka dake cikin karamar hukumar Rafi.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu sama da mako guda ke nan mutanen na kai hare hare a kauyukan Rafin Sany da kuma Alawa tare da yin awan gaba da
tarin dabbobi da duk wata dukiya da
suka yi karo da ita.

Baicin sace dukiyoyi suna yiwa mata fyade har da kashe duk wadanda suka yi masu taurin kai.

Malam Namadi Gajere dake zaune a
yankin Rafin Sanyi wanda lamarin ya shafa yayi karin haske;

“Yace an kwashe shanunsa kana an shiga gidansa an yi binciken kwakwaf.
Hatta jariri dake kwance kan gado sai da suka saukar dashi suka kwashe shimfidar”.

Wani dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar karamar hukumar Rafi
Onarebul Danlami Bako yace maharan sun yi kama da ‘yan kungiyar Boko Haram.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Yace basu da wani imani.

Yadda ‘yan Boko Haram su keyi haka ma su din su keyi.

Ya kira a taimakawa mutanen yankin domin suna cikin wani mawuyacin hali.

Ita ma gwamnatin jihar tace masu
aikata ta’asar baki ne da suka shiga
jihar kamar yadda kwamishanan
labaran jihar Mr. Jonathan Batsa ya
fada.

Shugaban karamar hukumar Rafi
Onarebul Gambo Tanko yace sun
gayyaci sojoji zuwa yankinsu.

Su ma ‘yansanda sun ce suna iyakar
kokarinsu domin kawar da miyagun
mutanen.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.