An Tsige Babachir Lawan Daga Matsayin Shugaban Kwamitin Tantance Shugabannin Hukumomin Gwamnati

0

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya tsige Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal daga shugabancin kwamitin da ke tantance sunayen wadanda za a nada shugabannin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya.

Shugaban kasar ya kuma maye gurbinsa da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Rahotanni na nuna cewa shugaban kasar ya dauki wannan mataki ne a sakamakon koke koken da ake ta gabatarwa kan yadda Sakataren gwamnatin ke tafiyar da ayyukan sa a kwamitin.

An dai nada kwamitin ne dama domin su na taimakawa wajen zakulo wadanda suka cancanta su rike mukamin gwamnati.