An Shiga binkicen Matar tsohon shugaban kasar Nigeria

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a shiga wani binciken sirri akan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da matarshi Patience Jonathan akan zargin cewa suna da hannu dumu dumu a fashe fashen bututunan mai da ke faruwa a yankin Niger Delta. Jaridar Premium Times ta Rahoto cewa ta samu kwararan bayanai daga wata majiya daga gwamnati cewa binciken da ake ta yi akan rikicin yankin Niger Deltan na nuna cewa tun lokacin mulkin Jonathan dab da lokacin zaben 2015, wasu daga cikin tsoffin ‘yan tada kayan baya da ke kusa da tsohon shugaban kasara suka dana boma bomai a bututunan man da ake fasawa yanzu. Majiya wacce ta bukaci kada a bayyana sunan ta ta bayyana cewa an dana bama baman ne a shirin hargitsa kasar idan tsohon shugaban kasar ya fadi zabe. Sai dai da hakan ya tabbata, sun watsar da shirin a cikin rudani. Majiyar ta ci gaba da cewa, an sabunta shirin ne bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shiga binciken da yawa daga cikin wadanda ke goyon bayan shirin tun farko. A lokacin ne kungiyar Niger Delta Avengers ta tsiro ta fara fashe fashen bututunan mai. Tun da sun riga sun dana boma boman, sai dai kawai su shirya yadda zasu tada su daga nesa, a duk lokacin da su da masu daukan nauyinsu suka ga dama, majiyar ta ce. Shirin shine a lalata tattalin arzikin kasar ta yadda za’a tilastawa gwamnatin Buhari ta yi amfani da mafita irin ta siyasa wajen warware zargin badakalar kudin da ake yiwa wadanda ake tuhuma. Masu yi wa gwamnatin tarayya bincike akan al’amarin a yanzu haka suna yunkurin gano ko har yanzu akwai wasu bututunan man da boman boman da aka dana masu bai ta shi ba, a warware su. Haka zalika masu binciken su tattare jerin sunayen duk wadanda aka koyawa fasahohi da suka shafi ayyukan kungiyar ‘yan tada kayan bayan a karkashin shirin afuwa da aka yi abaya. Jaridar Premium Times ta yi kokarin jin ta bakin tsohon shugaban kasar kafin a wallafa wannan bayani, amma hakan bata samu ba. Haka kuma ta yi kokarin jin ta bakin mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai, hakan ma bai yi wu ba. Sai dai ta samu jin ta bakin mai magana da yawun shugaban kasar Laolu akande inda ya bayyana cewa yana sane da bincike ya zurfafa akan fashe fashen bututunan mai, sai dai ba zai iya fadar abunda binciken ya kunsa ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.