An kona Gidan Dan Takarar Gwamnan Kano na-PDP

0 37

Click to subscribe my channel

Yayin da babban zaben shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, farfajiyar siyasar Najeriya na kara dumama, domin kuwa a yanzu haka abin ya haura dumama, har ta zafafa, kuma wannan shine babban abinda ake tsoro ya faru a siyasar.

A duk lokacin da aka ce siyasa ta yi zafi, za’a ga cewa abokan hamayya basa jituwa, hamayyar kanta ta sauya ta koma kiyayya kararara, sau dayawa hakan ka iya sabbaba asarar dukiya, da kuma asarar rayuka a sakamakon tashin hankalin da hakan ke haifarwa.

Da yammacin ranar Lahadi, 10 ga watan Feburairu ne wasu miyagun fusatattun matasa suka kai farmaki zuwa wani gida mallakin dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Abba Kabir Yusuf, inda suka kone gidan kurmus.

KARANTA WADANNAN;
1 of 104

Shi dai wannan gida yana nan ne a unguwar Chiranchi, kuma majiyar arewaclass.com ta ruwaito Abba Yusuf ya gina wannan gida ne domin gudanar da tarukan siyasa, da na bukukuwa a cikinsa, a takaice dai jama’a ke amfani da gidan fiye da shi.

Sai dai wasu masana siyasar Kano suna ganin kone gidan Abba baya rasa nasaba da nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar data gudanar a jahar Kano a ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha.

Dubun dubatan al’ummma ne suka yi tururuwa tare da yin fitar farin dango zuwa filin wasan domin tarbar Atiku Abubakar da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a dalilin haka wasu mutane bakwai suka fadi sumammu saboda tsabagen turmutsitsin jama’a.

©legit

Click to subscribe my channel