An kayade kayan aure a Dabbata

0

Dattijai a karamar hukumar Danbatta da ke Kano sun nuna halin dattako inda bayan lura da suka yi da ta’azzarar da farashin aure ya yi
karamar hukumar da ma kasr Hausa baki daya, dattijan suka kafa wani kwamiti da zi saukaka nema da yin aure a fadin karamar hukumar ta Danbattan Malam Ado Muhammad wanda shine mataimakin kwamitin na tabbatar da saukaka nema da yin aure na karamar hukumar ta
Danbatta ya bayyana wa gidan rediyon Freedom cewa, kwamitin ya fitar da tsaidajjen farashin aur wanda ya ke kamar haka:

Kayan lefe:

turmin atamfa da shadda 6
rigar mama 6
dan kamfai 6
fatari 6
takalmi, jaka, sarka da yari 6
kayan kwalliya suma kar su wuce 6 din… da dai sauran abubuwan da ke zubawa a akwatin lefe na wani adadi da ba zai takura ba

Sadaki

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Sadaki kar ya wuce Naira dubu 20
Malam Ado Muhammad ya bayyana cewa dattijan Danbatta sun dauki wannan mataki ne sakamakon ganin yadda ‘yan mata zunduma
zunduma ke yawo a gari babu masansani da kuma yadda samari madaka kato ke ta yawo
babu aure duk saboda tsadar aure.

Wani abu kuma da ya ke nema ya zama ruwan dare a karamar hukumar shi ne yawaitar fyade
wanda shi ma bincike ke nuna rashin aure ne sakamakon tsadarsa ya kawo hakan Kwamitin tare da taimakon hukumar Hisba ta
karamar hukumar ta Danbatta ya dau alwashin tabbatar da wannan ka’ida a sako da lungun
karamar hukumar ta Danbatta
Shi ma babban daraktan hukumara ta Hisba ta Kano, Alhaji Abba Sufi wanda shi ma dan karamar hukumar Danbatta ne, ya dada
tabbatar da wannan tsari tare da nuna goyon bayansa dari bisa dari da kuma yin alwashin taimakawa wajen ganin karamar hukumar
Danbatta ta zama abin koyi a wannan fuskar.

Sai dai a yayin da samari ke murna da wannan tsari, su kuma ‘yan mata a daya bangaren ba su yi amanna da wannan tsari ba inda muka jiwo wata budurwa na cewa wai an
karya musu farshi da daraja, inda har ta ke cewa tun bayan fitar da wannan sharadi samari ke zolayarsu da sun gansu inda suke
kiransu da “Atamfa 6” da di sunaye
makamantan hakan