An kashe mutane hamsin a masallaci – Adamawa

0

Akalla mutum 50 suka mutu bayan wani ya kai harin kunar bakin wake a wani masallacin cikin garin Mubi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ce ta tabbatar wa BBC Hausa cewa akalla mutum 50 sun mutu a harin.

Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Dan kunar bakin waken yana tsakiyar jama’a ne lokacin da ya tayar da bam din shi bayan an tayar da Sallah.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga Sashen Hausa na BBC, kwamishinan watsa labarai na jihar Adamawa, Ahmed Sajo, ya ce hukumomi ba za su iya tabbatar da iya adadin wadanda suka mutu a harin ba tukunna.

Wannan ne karon farko da aka kai hari da ya kai haka muni garin na Mubi tun bayan sojojijn Najeriya sun kwato garin daga hannun ‘yan Boko Haram.

Mayakan Boko Haram dai sun kwace garin na Mubi ne a shekarar 2014, amman daga baya sojojin Najeriya suka kwato garin daga hannunsu