An kara tsanar Bakar fata a burtaniya

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wani sabon rahoto da aka fitar a Burtaniya, ya nuna cewa bakar-fata da kabilu marasa rinjaye a kasar na fuskantar mummunan rashin daidato da wariya a wasu yankuna, kuma lamarin ya kara munana cikin shekaru biyar da suka gabata. Rahoton na hadin-gwiwa da hukumar daidaito tsakanin al’uma da hukumar kare hakkin bil’adama ta Human Rights suka fitar , ya bayyana yadda aka samu karuwar kai aikata muggan laifukan da suke nuna tsana tun bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a watan Yunin da ya wuce. Rahoton ya yi hasashen cewa adadin bakar-fatan da ke fuskantar barazanar hallakawa da yanke musu hukuncin kisa ya rubanya da kashi uku. Sai dai a nata bangaren, gwamnatin Birtaniya ta ce tana kokarin yin garanbawul a bangaren shari’ar kasar, kuma hakan za ta faru nan ba da jimawa ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.