An kama yan boko Haram a kano

0

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce ta kama ‘yan Boko Haram guda 3 a jahar Kano a yayin da suke yunkurin shirya yadda za su tada boma bomai a lokacin bukukuwan karshen shekara.

A wata sanarwa da jami’in hukumar Tony Opuiyo ya fitar a jiya Juma’a, hukumar ta ce a ci gaba da yakin da ta ke da ta’addanci, ta kama mutane uku, Samaila Muhammad, Sanusi Musa da Hudu Muhammad, a kauyen Dirbunde da ke karamar hukumar Takai a jahar Kano.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Opuiyo ya ce ‘yan ta’addan uku sun gama shirye shiryen tada boma bomai a wasu jahohin Arewa maso gabashin kasar nan a watan tun a watan Nuwanbar domin su hargitsa duk wani yunkuri na yin bukukuwan karshen shekara.

Haka kuma hukumar ta ce ta kama wani Sani Digaru tare da Muhamma Ali a ranar 25 ga watan disambar a jahar Gombe dauke da naira miliyan biyu da suke yunkurin su yi amfani da shi wajen shirya tashe tashen hankula a jahar Yobe da Bauchi a lokacin bukuwan kirsimeti da karshen shekara.