An kama shugaban yan ta’ada a Lagos

0

‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke shugabannwata kungiya, da ke shirya yadda za su tarwatsa babbar gadar sama a birnin Legas.

Jami’an sun kara da cewa sun kuma gano ababen fashewa, da makamai a lokacin da suke gudanar da bincike.

‘Yan sanda sun yi ikirarin cewa mutumin da ake zargin, wani jagora ne na masu gwagwarmaya da makamai, kana kwararre ne kan hada abubuwa masu fashewa.

An yi zargin cewa mutumin mai shekaru arba’in da uku, ya shirya tarwatsa babbar gadar nan ce ta Third Mainland Bridge, wadda ta hada yankinharkokin kasuwanci da ke tsibirin, da kuma sauran sassan babban birni mai hada-hada.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

‘Yan sanda sun ce suna kuma farautar sauran ‘yanbkungiyar da ke shirin tada zauna tsaye.

Wani jami’i ya ce mutumin da ake zargin yana da alaka da kungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Niger-Delta mai arzikin mai.

Yankin dai yana fama da hare-hare wadanda suka yi sandiyar raguwar hako man fetur da Nigeria ke yi har kashi daya cikin uku, na adadin man da kasar ke hakowa.