An kama shugaban kwamitin wasan Oliampic

0
‘Yan sanda a Brazil sun kama shugaban kwamitin sa ido kan wasanni Olympics, Patrick Hickey a Rio, yayin wani bincike kan sayar da tikitin gasar Olympics din ta barauniyar hanya. Mista Hickey shi ne kuma shugaban Majalisar Olympics na jamhuriyar Ireland. Ana zargin shi ne da bayar da tikitin da aka warewa ‘yan kwamitin Olympics ga wasu ‘yan cuwa-cuwa da suka sayar da shi a kan farashi mai tsada a kasuwannin bayan fage. An dai kai Mista Hickey asibiti bayan da ya ce yana bukatar ganin likita. Kafofin yada labarai a Brazil sun bayar da rahoton cewa tsare jami’in ba zai rasa alaka da wani dan Ireland ba, kuma darakta a wani kamfanin karbar bakin wasannin kasashen waje, wanda shi ma ke hannun ‘yan sanda.
KARANTA WADANNAN;
1 of 236