An daure ‘yan damfarar da suka kafa bankin bogi a China

0 1

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

An daure wasu mutane biyu a lardin Nanjing na kudancin kasar Sin bayan samunsu da laifin kafa
banki na bogi inda suka damfari mutane miliyoyin daloli.

Kafafen watsa labaran kasar sun ce mutanen sun yaudari abokan huldarsu ne da alkawurran samun
riba ninkin-ba-ninkin idan suka ajiye kudi a bankin.

Rahotanni sun ce sun tsara ginin bankin na bogi ne ya yi kamar daya daga cikin bankuna mallakar
gwamnatin kasar ta Sin.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

”Ma’aikatansu da ke saka kaya na bai-daya wato Uniform da kuma takardun rubuta kudin da mutum
zai a jiye, duk sun yi kama da na wasu bankunanbkwarai da ake da su a kasar; kodayake bankin
nasu na bogi ne,” In ji wakilin BBC a birnin Beijing.

A yanzu dai mutanen na can a daure – daya na tsawon shekaru tarabdayan kuma na tsawon shekaru tara da rabi.

Kafafen watsa labaran gwamnati sun ce mutanen biyu, Zeng da He, sun damfari abokan huldar na
su dala miliyan sittin.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram