An damke wani da kan mutum a jihar lagos

0 3

Click to subscribe my channel

Rundunar ‘yan sandan jahar Lagos ta samu kan mace a gidan wani mai maganin gargajiya a yankin Imota da ke kusa da Ikorodu a jahar Lagos.

Majiya daga sashen bincike akan manyan laifuka na rundunar ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN cewa an kama wani mutum mai suna Emmanuel a gidan mai maganin wanda ake kira Jami’u.

Ya ce sai dai ba su samu nasarar kama shi kan shi Jami’u ba saboda ya tsere.

Makotan Jami’u ne dai suka kaiwa ‘yan sanda rahotan cewa suna jin wani wari ya na fitowa daga gidan shi.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Da ‘yan sanda suka yi bincike a gidan ne suka gano kan wata mata, wanda har ya fara rubewa.

Emmanuel ya fadawa ‘yan sanda cewa Jami’u ne ya taya shi samo kan domin ya hada masa maganin kariya daga matsafan Badoo da suka addabi yankin.

‘Yan sandan sun ce za su gurfanar da Emmanuel a gaban kuliya yayin da suke ci gaba da neman Jami’u.

Source: alummata.com

Click to subscribe my channel