An ci tararar matar da ta kai rahoton cinhanci

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wata kotu a Senegal ta ci tarar wata mata $250 tare da yanke mata hukuncin ɗaurin wata guda na jeka ka gyara halinka, saboda ta bai wa wani ɗan sanda cin hanci, duk kuwa da cewa ta naɗi bidiyosa ne. Matar ta ɗauki bidiyo ɗan sandan a asirce yana neman ta bashi hanci saboda ta keta dokar hanya, kuma ta bashi dala biyar. Bidiyon wanda ta wallafa a shafin sada zumunta ya nuna ɗan sandan ya karɓi kudin, sannan ya tauna takardar laifin da ya rubuta mata na laifin keta dokar hanya. Sai dai shi ma ɗan sandan ba a bar shi haka ba, domin an ci tararsa $250 da kuma ɗaurin wata biyu na jeka ka gyara halinka.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.