Amurka ta kori Jami’an diflomasiyyar Rasha 35 bisa zargi kutse

0

Gwamnatin Amurka ta kori jami’an diflomasiyyar Rasha 35 daga kasarta bisa zargin yin katsalandan cikin zaben shugaban kasar na watan jiya.

An dai ba su sa’oi 72 sun fice daga kasar kuma za a rufe wasu cibiyoyi biyu da suke amfani da su wajen tattara wa Rasha bayanan sirri.

A cikin wata sanarwa Shugaban Barack Obama ya kira wannan matakin a zaman wanda ya zama dole kuma ya dace a zaman martani ”ga kokarin yi wa muradun Amurka lahani” yana mai cewa ya kamata kowane dan kasar ya yi hattara da aikace-aikacen Rasha.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Tun ba yau ba dai shugaba Obama ya sha alwashin daukar mataki kan Rasha bisa zargin cewa ita ce ta bayar da umarnin yin kutse a akwatunan sakonnin e-mail na jam’iyyar Demokrat da kuma ofishin kamfe na Hillary Clinton.

Sai dai Rasha ta musanta zargin wanda ta kira maras tushe.