Amina daya daga cikin yan matan chibock na kewar mijinta dan Boko haram

0 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daya daga cikin ‘yan matan nan na Chibok fiye da 200 da Boko Haram ta sace, wadda aka ceto ta, Amina Ali ta ce tana kewar ‘mijinta.’ A wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Reauters a Abuja, a ranar Talatar da ta wuce, yarinyar ta ce tana son uban ‘yarta ya san cewa tana tunaninsa. “Ina so ya san cewa ina tunaninsa, sabo da an raba mu ba wai yana nufin na daina tunaninsa ba ne.” Wasu ‘yan kato da gora ne suka ceto Amina Ali da wani wanda ta ce minjinta ne a wani daji da ke jihar Borno. Kuma ita ce ta farko daga aka ceto daga cikin ‘yan mata ‘yan makaranta fiye da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace a shekarar 2014. Tun bayan ceton ne dai gwamnatin Najeriya ta ajiye ta da ‘yarta a wani gida domin kula da su. Sai dai babu wanda ya san a inda mutumin da ta bayyana cewa mijinta ne, wanda kuma sojin kasar suka ce dan Boko Haram ne yake ba. ‘Yar Chibok din ta kuma bayyana cewa tana son ta koma gida, sai dai bata san ranar da za ta koma ba. Haka kuma a yanzu ba ta tunanin komawa makaranta, amma abu ne da zata duba bayan ta koma gida.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.