Amaida majalissar Nigeria ta wuccin gadi

0

Advertisement

Tsohon Shugaban kasan Nijeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya baiwa gwamnatin Nijeriya shawarar a mayarda Majalisun Dokokin kasar na wucin gadi domin a rage makudan kudaden da ake kashewa a kansu, a kuma kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye majalisun. IBB ya fadi haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba don murnar cikarsa shekaru 75 a duniya. Wannan kalamai na tsohon shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin majalisar wakilai da ke faruwa sakamakon badakalar kasafin kudi ta dau zafi. Yan Nijeriya dai suna nan suna zuba idon ganin yadda abun zai kaya, musammam ma irin matakin da mahukunta za su dauki mataki akan al’amarin.

Leave a Reply